Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Zaben shi ne irinsa na farko tun bayan mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.
Bayanai daga kasar sun ce zaben ‘yan gudana cikin lumana.
A cen baya dai akan sanar da sakamakon zaben a washe garin kada kuri’ar.
Sama da ‘yan kasar dubu 960 ne aka tantance zasu kada kuria’a a zaben, wanda ake wa kallon zakaren gwajin dafi ga jinjirar demokuradiyyar kasar.
‘Yan takara shida ne suka fafatawa a zaben ciki har da shugaba mai barin gado Adama Barrow da kuma tsohon mataimakinsa Ousainou Darboe, kana madugun ‘yan adawa na kasar.
342/